Tattalin arzikin ƙasashen Sahel na farfaɗowa sannu a hankali-IMF

Tattalin arzikin ƙasashen Sahel na farfaɗowa sannu a hankali-IMF

Ofishin asusun da ke kula da nahiyar Afrika ne ya bayyana hakan, yana mai cewa an sami wannan ci gaba ne sakamakon aiwatar da shawarwarin da yake baiwa ƙasashen.

A wani rahoto da IMF ɗin ya fitar, ya ce ƙaruwar talauci, ƙarancin ayyukan yi, gwamnatin ci barkatai mara tsari na cikin manyan abubuwan da waɗannan ƙasashe zasu yaƙa don kawo  ƙarshen matsin tattalin arziki.

Asusun na IMF ya ce har yanzu hasashen ci gaban tattalin arzikin da waɗannan ƙasashe zasu samu na nan kan kaso 3.6 cikin 100 a shekarar 2025.

A wani bincike na daban da asusun ya gabatar ya nuna cewa bashin da ake bin waɗannan ƙasashe ya ragu matuƙa da gaske, to sai dai kuma a iya cewa wannan ƙididdiga ta ci karo da wadda ƙasashen ke fitarwa da ke nuna cewa bashin da yayi musu katutu na ƙaruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)