
Shugabanin za su gudanar da taron ne a wani lokaci da ake fuskantar tashin hankali a ƙasashe da dama na Afrika da suka hada da Sudan,DRCongo.
A jiya juma’a ne yan tawayen M23 da ke samun goyan bayan dakarun Rawnda suka kwacve ikon Bukavu,lamarin da ya hana shugaban kasar ta DRCongo halartar wannan taro.
A daya gefen taron shugabanin zasu tanttance mutumin da zai gaje Moussa Faki Mohammed ɗan kasar Chadi da ya rike mukamin shugaban zartaswa na hukumar tsawon shekaru takwas.
Wasu daga cikin jami’an diflomasiya na Afrika irinsu Mutari Ali Daura na ganin cewa ,wasu daga cikin manyan ayuka da Shugabanin zasu fi mayar da hankali a kai sun hada da batun tsaro da tattalin arziki.
01:15Taron kasashen Afrika
Babban magatakardar Majalisar Dimkin Duniya Antonio Guterres a yau Asabar ya bukaci a mutunta ‘yancin yankin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo tare da kaucewa jefa yankin cikin wani yaki.
An ga shugaban Rwanda Paul Kagame a zauren taron, amma shugaban DR Congo Felix Tshisekedi bai halarci taron ba yayin da 'yan M23 suka mamaye yankin kasarsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI