Manyan Sojin na Rasha waɗanda suka gwabza mabanbantan yaƙi a ƙasashen Libya da Syria, suna cikin Sojin hayar Wagner da yanzu haka ke yaƙi da ƴan ta’adda a Sahel, bayanan na Reuters sun ce sun rasa rayukansu ne a faɗan da suka gwabza da ƴan tawayen Mali cikin watan Yulin da ya gabata.
A cewar Reuters bayan tattaunawa da ahalin Sojojin da kuma wallafe-wallafen da makusantansu ke yi a shafukan sada ne aka samu tabbacin mutuwar dakarun waɗanda ke aiki ƙarƙashin Wagner, duk da cewa kawo yanzu gwamnatin Rasha ba ta ce komai game da lamarin ba.
Mutuwar waɗannan zaƙaƙuran Sojoji ya jefa aikin kamfanin Wagner cikin haɗari musamman a ƙokarin da ya ke na tabbatar da tsaro da kuma yaƙi da ta’addanci a ƙasashen Sahel biyu da ke ƙarƙashin mulkin Soji.
Bugu da ƙari kisan sojojin ya sa fargabar yiwuwar sake ƙarfin ƙungiyoyin ta’addanci da ke iƙirarin jihadi bisa taimakon Al Qaeda a ƙasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar.
A ɓangare guda gazawar Sojin na Wagner ya sanya fargabar yiwuwar ita ma Rasha ta fuskanci tutsun ƙasashen na Sahel waɗanda a baya-bayan nan aka ga yadda suka yi baram-baram da ƙasashen yamma ta hanyar korar dakarunsu da na Majalisar ɗinkin duniya daga ƙasashen bayan gaza daƙile hare-haren ƴan ta’adda.
A cewar Reuters cikin waɗannan sojoji akwai zaƙaƙurai 23 da aka gano fuskarsu waɗanda suka gwabza yaƙi wajen ragargazar Bakhmut a Ukraine ƙarƙashin jagorancin Yevgeny Prigozhin ma'assasin Wagner, haka zalika da damansu sun tsallake yaƙe-yaƙen Libya da Syria ko da ya ke akwai wasu ƙusoshin yaƙin biyu da jaridar ke cewa suna tsare a hannun ƴan tawayen na Tuareg.
Wasu bayanai sun ce bayan mutuwar Prigozhin ma’assasin Wagner a watan Agustan bara, galibin mayaƙan kamfanin sun koma ƙarƙashin ikon ma’aikatar tsaron Rasha ta yadda suka koma yaƙi domin kare manufofin ƙasar ƙarƙashin wata runduna da aka sanyawa suna Africa Corps.
Har zuwa yanzu ma’aikatar tsaron Rasha da ta harkokin waje da ma kamfanin na Wagner basu ce komai game da mutuwar dakarun a Mali ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI