Tarayyar Afirka (AU) ta bayyana cewa, ta gamsu da yadda gwamnatin Somaliya ta sanar da za a gudanar da zabe nan da kankanin lokaci a kasar.
Sanarwar da aka fitar daga Tarayyar ta ce,
"Shugaban Tarayyar Afirka Musa Faki ya gamsu matuka kan taron da Shugaban Kasar Somaliya Mohammed Abdullahi Farmaaju ya bukaci a gudanar a zauren majalisar dokoki inda aka amince kan za a yi aiki da yarjejeniyr 17 ga Satumba tare da gudanar da zabe nan da wani dan lokaci."
A ranar 8 ga Fabrairu Shugaban Kasar Somaliya da ake dade ana rikici game da zabe a cikinta ya samu nasarar sake ci gaba da zama a kan mulki duk da cikar wa'adinsa wanda hakan ya tunzura wasu 'yan adawa da shugabannin jihohi.
A ranar 17 ga Satumban 2020 Shugaba Farmaaju ya gana da Shugabannin jihohi inda aka amince da za a gudanar da zabe a fadin kasar amma sakamakon rashin daidaitawa a Hukumar Zabe ya sanya ba a bayyana yaushe za a yi zaben ba.