Tarayyar Afirka ta fara rarraba allurar riga-kafin Corona (Covid-19) da ta saya daga wajen kamfanin Johnson&Johnson na Amurka.
Shugaban Kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana cewa, a ranar Alhamis din na an fara rarraba allurar riga-kafin Corona da Asusun Samar da Corona ga Afirka ya sayo ga kasashe mambobin Tarayyar.
An tunatar da cewa, a watan Maris Asusun ya kulla yarjejeniyar sayen alluran riga-kafin Corona na Johnson&Johnson guda miliyan 400.
An sanar da cewa, daga ranar Alhamis din nan alluran za su fara isa kasashen nahiyar Afirka da dama, a wannan watan za a kai kwaya miliyan 6,4 inda nan da watan Disamba ake sa ran aika miliyan 50 ga kasashe mambobin Tarayyar Afirka.
Sanarwar ta bayyana an samar da wani bangare na alluran a masana'antar Johnson&Johnspn da ke Afirka ta Kudu.
Ya zuwa yanzu alluran riga-kafin Corona miliyan 103,5 kawai aka iya kaiwa kasashen Afirka mafi yawanci ta karkashin shirin COVAX.