Tanzania ta dakatar da jaridar da ta alakanta shugabar ƙasar da kisa

Ɗaya daga cikin hotunan bidiyo da jaridar The Citizen ta wallafa  ya nuna shugaba Samia Suluhu Hassan zaune tana kallon bidiyon cin zarafin da aka yi wa ƴan adawa haɗe da wasu da ba su ji ba basu gani ba.

Gabanin faruwar lamarin shugabar ƙasar ta fuskanci caccaka daga ciki da wajen Tanzania game da zarge-zargen da ake yi wa jami’an tsaron ƙasar da alhakin yin garkuwa tare da kashe wasu daga cikin jiga jigan jamiyyar adawa na ƙasar.

Tuni dai jaridar ta cire tallace-tallacen da ta wallafa, kana ta fitar da sanarwar da ke cewa manufarsu ita ce bayyana damuwar allummar ƙasar a game da matsalolin tsaro.

A jiya Laraba ne The Citizen da ke kan gaba daga cikin jaridun da ake walafawa da harshen Turanci a Tanzania ta fitar da sanarwar dakatar da ayyukanta na tsawon kwanaki 30 da hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta  Tanzaniya ta yi.

Tun a cikin watan Agustan da ya gabata ne dai, gwamnatin Samia Suluhu Hassan ta haramta manyan gangami biyu da jam’iyyar Chadema ta ƙaddamar, sannan ta sanar da batun tsare shugabannin jam’iyyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)