Tankokin yaƙin Rasha fiye da 100 sun isa Mali daga Syria don ƙarfafa Wagner

Tankokin yaƙin Rasha fiye da 100 sun isa Mali daga Syria don ƙarfafa Wagner

Bayanai sun ce tun bayan faɗuwar gwamnatin Bashar al-Assad a Syria, Rasha ta fara laluben yankin da za ta jibge dakarunta waɗanda a baya ke a sansanin Moscow na Damascus, waɗanda kuma su ne ke kula harkokin ƙasar a Afrika dama gabas ta tsakiya.

A cewar wasu majiyoyi motocin yaƙi fiye da 100 ne suka isa Bamako a ranar 17 ga watan da muke na Janairu ciki har da tankokin yaƙi ƙirar T-72B3M da BMP-3 baya ga motocin yaƙi ƙirar BTR-82A 8×8 da kuma Spartak da Linza kana Tiger 4×4 masu silke.

Kafin yanzu akwai bayanan da ke nuna cewa, Rasha ta kwashe wani ɓangare na sansanin Sojinta zuwa Libya, tun bayan faduwar gwamnatin ta Assad a watan Disamban bara.

Alamu na nuna cewa Rasha na son ƙarfafa dakarunta na Sojin hayar Wagner waɗanda ke aiki da gwamnatocin ƙasashe da dama a nahiyar ta Afrika ciki har da Mali wadda ko a watannin baya-bayan nan aka ga yadda ƴan ta’addan ƙungiyar JNIM mai biyaya ga alqaeda ta hallaka da dama daga cikinsu.

Wannan bayanai dai na zuwa ne a dai dai lokacin da shugaban na Mali Kanal Assimi Goita ke sanar da shirin ƙasar na samar da kamfanonin ƙera makamai mallakinta a cikin gida don kaucewa fita ƙasashe neman makaman.

Mali na sahun ƙasashen Sahel da ke ci gaba da fuskantar hare-haren ƙungiyoyin ƴan ta'adda da ke iƙirarin jihadi wanda ke barazana ga tsaro da zaman lafiyar al'ummarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)