Tanadin dokokin Kamaru idan shugaba ya yi ɓatan dabo na tsawon lokaci

Tanadin dokokin Kamaru idan shugaba ya yi ɓatan dabo na tsawon lokaci

Paul Biya mai shekaru 91 da ya fara jagorantar Kamaru tun daga shekarar 1982 rabon da a ganshi a bainar jama’a tun ranar 8 ga watan Satumban da ya gabata, lamarin da ya sanya fargabar yiwuwar ko dai ya mutu ko kuma yana fama da rashin lafiya, duk da cewa mahukuntan ƙasar na ci gaba da musunta wannan jita-jita baya ga haramta tattaunawa kan batun lafiyar shugaban a kafafen yaɗa labarai.

Duk da yadda mahukunta na Kamaru suka tsaurara matakan da suka kange manema labarai daga tattaunawa kan wannan batu, al’ummar ƙasar na ci gaba da ɗiga ayar tambaya kan ko me ka iya faruwa a wannan yanayi da babu masaniya kan inda shugaban ya ke.

Tanadin kundin tsarin mulkin Kamaru na 1996 ya umarnin miƙa ragamar ƙasa a hannun Firaminsita a lokacin bulaguron shugaba har zuwa dawowar shugaban amma na gajeran wa’adi.

Sai dai a yanayi na mutuwa ko ajje aiki ko kuma yanayi na gaza iya tafiyar da gwamnati ko kuma ɓatan dabon shugaban na kwanaki 40 kai tsaye za a miƙa mulki ga shuagban majalisar dattijai wanda zai zama shugaban riƙon ƙwarya gabanin zaɓe, wannan dalili ya sanya Kamaru samar da mataimakan shugaban Majalisa har 5.

Ƙarƙashin kundin tsarin mulkin na Kamaru idan har shugaba ya gaza bayyana har na tsawon kwanaki 120 kai tsaye ya zama wajibi a kira zaɓen gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)