
A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne dai ofishin baitalmalin Amurka, ya ƙaƙaba wa James Kabarebe, takunkumi saboda rawar da ake zargin ya taka a matsayin wakilin gwamnatin Rwanda a ƙungiyar ƴan tawayen M23, duk da cewa bai yi magana kai tsaye kan matakin da aka ɗauka a kansa ba.
Haka nan itama Birtaniya ta ce za ta dakatar da wasu tallafin da take bai wa Rwanda kai tsaye, tare da ƙaƙaba mata wasu takunkuman diflomasiyya, har sai an samu ci gaba wajen kawo ƙarshen rikicin da kuma janye dakarun sojojin Rwanda daga yankunan Congo, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce sun kai dubbai.
Itama Ƙungiyar Tarayyar Turai EU ta bayyana cewa za ta sake duba yarjejeniyar ta da Rwanda, kan abinda ya shafi ma'adanai, sakamakon dangantakar da ke tsakanin Kigali da ƴan tawayen na M23.
Sai dai Rwanda ta sha musanta dukkanin waɗannan zarge-zargen da ake mata na taimaka wa ƴan tawayen M23 da matakai, sannan ta ce sojojinta na kare kansu ne daga hare-haren sojojin Congo da ƙungiyoyin ƴan sa kai masu adawa da Kigali.
Kawo yanzu dai ƴan tawayen M23, da ke samun goyon bayan Rwanda, sun ƙwace manyan birane biyu a gabashin Congo a cikin watannin nan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI