Sudan ta yi watsi da rahoton da ke nuna fantsamar yunwa sassan ƙasar

Sudan ta yi watsi da rahoton da ke nuna fantsamar yunwa sassan ƙasar

Wani bincike da Hukumar Hadaka da Samar da Abinci ta IPC ta gudanar, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi amfani da shi a makon da ya gabata, ya ce yaƙin da ake yi tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF ya sanya mutane dubu 638 na fuskantar yunwa, yayin da wasu miliyan 8.1 ke gab da fuskantar matsalar.

To sai dai wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar da a matsayin martani kan wancan rahoto, ta ce gwamnatin mulkin sojin ƙasar ta yi watsi da rahoton da IPC ta fitar dangane da halin da ake ciki na yunwa a wasu sassan ƙasar.

Sanarwar ta bayyana rahoton a matsayin mara tushe tare da zargin hukumar ta IPC da gazawa wajen bin ka'idar tara bayanai.

Gwamnatin ta Sudan ta ce tawagar jami'an hukumar ba ta samu damar samun sahihan bayanai a binciken nasu da suka gudanar ba, sannan ba ta tuntubi waɗanda ɓangaren gwamnati kafin ta fitar da rahoton ba.

Rahoton dai ya tabbatar da gargaɗin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta shafe tsawon lokaci tana yi wa ɓangarorin dda ke rikici da juna a ƙasar, game da halin da matsananciyar yunwar da ka iya mamaye ilahirin sassan ƙasar, ko da ya ke gwamnati ta haramta fitar da duk wasu bayanai masu alaka da halin da jama'arta ke ciki ga duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)