Ministan Harkokin Wajen Sudan Umar Kamaruddin ya bayyana cewar kasar ta amince da sasantawa da Isra'ila amma kuma akwai bukatar dole sai bangaren dokoki ya amince.
A sanarwar da Kamaruddin ya fitar ga kamfanin dillancin labarai na Sudan ya ce, mun amince da sasantawa amma kuma sai majalisar dokoki da za a kafa ta amince, wannan mataki zai fara aiki bayan samar da kundun tsarin mulki.
Kamaruddin ya kuma ce akwai matakai da yawa da aka dauka amma ba za su fara aiki ba sai majalisar dokoki ta amince da su, abu mafi muhimmanci shi ne amincewa da sasantawar kasashen 2.
Ministan ya ce sasantawa da Isra'ila zai habaka kasarsu a bangarorin tattalin arziki, kimiyya da fasaha da kasuwanci.