Sudan ta Kudu ta jinkirta babban zaɓen ƙasar da tsawon shekaru biyu

Sudan ta Kudu ta jinkirta babban zaɓen ƙasar da tsawon shekaru biyu

Wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasar Salva Kiir ta ce, sai a watan Disamban shekarar 2026 za a gudanar da zaɓen, wanda tun da farko aka tsaida za a gudanar a watan Disamban wannan shekarar.

A cikin sanarwar, babban minista a majalisar ministocin ƙasar, Martin Elia Lomuro ya ce jinkirta zaɓen ya zama wajibi duba da cewa ba a kammala mahimman abubuwan da ake buƙata don gudanar da zaɓen ba, yana mai cewa an bi shawarar hukumar zaɓe da ɓngaren tsaro ce wajen ɗaukar wannan mataki.

 

Kafin sanarwar ta ranar Juma’a, Sudan ta Kudu na shirin sake naɗa waɗanda za su jagoranci gwamnatin riƙon ƙwarya, waɗanda za su haɗa da jagora mai ci Salvada Kiir da mataimakinsa, Riek Machar, waɗanda dakarunsu suka gwabza da juna a yaƙin basasa.

Duk da cewa yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma shekaru 6 da suka wuce ta kawo ƙarshen yaƙin basasa da aka yi daga shekarar 2013 zuwa 2018 tsakanin shugaba  Salva Kiir da abokin hamayyarsa, kuma mataimakinsa, Riek Machar,  rikici tsakaninsu ya ci gaba da jinkirta zaɓe a ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)