Shugaban hukumar sadarwa ta kasar, Napoleon Adok, ya ce an dauki matakin ne, la’akari da yadda ake amfani da kafofin sada zumunta wajen tayar da zaune tsaye.
Masu amfani da layukan MTN da Zain a Sudan ta Kudu, b aza su damar shiga shafukan Facebook da TikTok ba, hadi da sauran shafukan sada zumunta har tsawon kwanaki 90, kamar yadda kamfanonin sadarwar suka bayyana a wata sanarwa.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, jama’a da dama sun gaza shiga shafukan Facebook da TikTok a Juba, babban birnin kasar.
Akalla ‘yan asalin Sudan 16 aka kashe, lokacin da tarzoma ta barke a Juba, cikin makon jiya.
Rikicin ya rikide zuwa kwasar ganima, inda matasa suka rika fasa shagunan ‘yan asalin Sudan, inda a wasu garuruwan ma sun kona musu gidaje, kamar yadda rundunar ‘yan sandan kasar ta tabbatar.
Tarzoma dai ta kasance a matsayin ramuwar gayya kan kisan da aka yi wa ‘yan Sudan ta Kudu a kasar ta Sudan a jihar El Gezira da ake zargin sojoji ne suka yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI