Kimanin mutune fiye da miliyan 6 ne ke fama da karancin abinci a yankin arewacin Dafur da dakarun RSF ke jagoranta, yakin da aka shafe kimanin watanni 16 ana gwabzawa tsakanin dakarun da sojojin kasar.
Tun a watan Fabrairun wannan shekara ne dai sojojin suka rufe iyakar Adre zuwa yankunan da dakarun ke wakilta,inda sukayi ikirarin cewa ana shiga da makamai ta iyakar.
Wakilan majalissar Dinkin Duniya a farkon shekarar nan sun zargi dakarun da samun makamai daga hadaddiyar Daular larabawa ta chadi sai dai dakarun da kasar sun karyata.
Yankin port sudan da gwamnatin kasar ta amince da bi domin shiga da kayayyakin agaji na daukar lokaci mai tsawo tare fuskantar matsaloli masu yawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI