Madugun 'yan adawa a Sanagal kuma Shugaban Jam'iyyar PASTEF Ousmane Sonko ya bayyana cewa, za a ci gaba da gudanar da zanga-zanga a fadin kasar.
Bayan sakin Sonko da aka yi, ya yi jawabi ga manema labarai a ofishin jam'iyyarsa.
Sonko ya ce, dole a biya diyya ga iyalan wadanda aka kashe a yayin zanga-zangar, kuma akwai bukatar a hukunta wadanda suka aikata ta'asar.
Dan adawa Sonko ya shaida cewa, da kansa zai shigar da kara kotun hukunta manyan laifuka ta duniya dangane da kashe mutane da aka yi a yayin zanga-zangar, ya kuma yi kira da a saki duk wadanda aka kama yayin gudanar da zanga-zangar.
Ousmane Sonko ya kuma ce lallai a nemo wasu mutane da ke dauke da makamai kuma suka rufe fuskokinsa wadanda ba jami'an tsaron kasar ba ne.
Ya ce, za a ci gaba da zanga-zanga har sai an saki dukkan fursunonin siyasar da aka kama, amma za a gujewa tayar da fitina.
Madugun 'yan adawar ya kara da cewa, an dade da fara juyinjuya hali, babu wanda ya isa ya dakatar da hakan, kuma za su ci gaba da gwagwarmaya har sai sun kai juyin juya halin zuwa shekarar 2024.
Shugaban Kasar Sanagal Macky Sall ya yi kira da a dakatar da zanga-zangar saboda an saki Sonko.
Sall ya ce, ya kamata kowa ya yi aiki da hankali, kuma kar wanda ya yi amfani da rkici wajen bayyana ra'ayinsa.
Shugaban na Sanagal ya kuma ce, a kyale bangaren Shari'a ya yi aikinsa game da tuhumar da ake yi wa Sonko.