Somalia ta zargi Habasha da 'shishigi' a kudancin Jubaland

Somalia ta zargi Habasha da 'shishigi' a kudancin Jubaland

Somalia da Habasha da ke makwabtaka da juna dai na takun-saka ne tun a watan Janairu 2024, tun bayan da kasar Habasha da ke da iyaka da kasar Somalia, ta kulla yarjejeniya da yankin Somaliland da ke ballewa daga Somalia, na ba da hayar wani yanki na gabar tekun ta, da tashar jiragen ruwa da kuma sansanin soji.

Somalia da aka jima ana fama da rikici,tarayya ce ta kasashe biyar masu cin gashin kan su

Puntland, Jubaland, Galmudug, Hirshabeelle da kuma Kudu maso Yamma da kuma gwamnatin tsakiya a Mogadishu,har ila yau wannan zargi na Somalia na zuwa ne jim kadan bayan sake zaben Jubaland na tsohon shugaban yakin kasar Ahmed Madobe, lamarin da ya harzuka gwamnatin tsakiya da ta yi fatan daidaita zaben da zabukan kasar nan gaba.

 Sanarwar da ma'aikatar yada labarai, al'adu da yawon bude ido ta Somalia ta fitar ta ce an tura dakarun Habasha zuwa gundumar Bulohawo da ke kudancin Gedo a jiya Juma'a, kafin daga bisani su yi arangama da al'ummomin yankin da kuma sojojin da suka dakatar da ci gaban. Ma'aikatar ta ce "Gwamnatin Somalia ta yi kakkausar suka ga munanan ayyukan da gwamnatin Habasha ke aiwatarwa a yankin Gedo na fara rikici tsakanin kabilun yankin.Addis Ababa dai ba ta ce uffan ba kan wannan zargi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)