Somalia ta dage cewa Habasha ba za ta kasance cikin sabuwar tawagar AU ba

Somalia ta dage cewa Habasha ba za ta kasance cikin sabuwar tawagar AU ba

Somaliya ta yi tsayin daka, kan cewa Habasha ba za ta kasance cikin sabuwar tawagar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka ba, yayin da kasashen biyu ke ci gaba da takun-saka a rikicin da ya barke a yankin ƙuryar gabashin Aifrka.

Tun a shekara ta 2007 ne dakarun Tarayyar Afirka ke fafata yaƙi da mayaka masu ikrarin jihadi na Al-Shabaab a Somaliya, da nufin mika alhakin tsaro ga dakarun kasa.

Rundunar AU na yanzu a Somaliya da aka fi sani da ATMIS wanda ya hada da sojojin Habasha kusan 3,000, za a kammala shi ne a karshen wannan shekara, domin maye gurbinsa da wani shiri da aka yi wa kwaskwarima mai suna AUSSOM.

Makwabtan biyu dai sun na takun-saka ne tun bayan da kasar Habasha da ba ta da kogi a watan Janairu ta kulla yarjejeniya da yankin Somaliyan da ke ballewa daga Somaliya, akan ba da hayar bakin tekun wani tashar ruwa da sansanin soji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)