Mutane da su ka fito kan titunan don nuna jin daɗinsu, sun bayyana farin ciki mara misaltuwa, a yayin da sojoji ke ta harbi a iska.
Yaƙin da aka fara a watan Afrilun shekarar 2023, tsakanin dakarun rundunar sojin Sudan da mayaƙan kai ɗaukin gaggawa na RSF, ya haddasa matsalar jin ƙai mafi girma a duniya.
Mamayar garin El Gezira da mayaƙa RSF su ka yi ya mayar da yankin mai yalwa da dausayi na ƙasar noma zuwa wani wuri da ke fuskantar barazanar ƙarancin abinci.
Ganau sun ce mayaƙan sun tada ƙauyuƙa, inda su ka ƙona dimbim gidaje.
RSF ta musanta wannan zargi, inda ta ce tana yaƙi ne da ƴan tsagera da ke aikata laifukan cin zarafi iri-iri.
Sake karɓe wannan gari da sojoji su ka yi zai yi matuƙar tasiri a ƙoƙarinsu na daƙile hanyoyin da RSF ke shigowa da makamai cikin Khartoum da gabashin ƙasar.
Ana iya ganin gawarwakin dakarun RSF a warwatse a tituna da kuma kan gadar da ta haɗe birnin da makwaftanta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI