Rundunar Sojin Sudan da kungiyoyin da ke mara musu baya sun kaddamar da wani farmaki a birnin jihar Al-Jazira Wad Madani dake da muhimmanci a fafatawar da suke yi da dakarun daukin gaggawa na RSF, inda suka shiga birnin bayan sama da shekara.
Inda dakarun sojin suka taya al'ummar Sudan murna a cikin wata sanarwa da suka fitar dake nuni da dakarun sun shiga birnin na Wad Madani da safiyar yau.
Tun a watan Afrilun shekarar 2023 ne faɗa ya ɓarke a tsakanin sojojin Sudan da dakarun na RSF, lamarin da ya kai ga abin da Majalisar Dinkin Duniya ta kira mafi muni a duniya a bangaren gudun hijira da kuma ayyana yunwa, a sassan kasar da ke arewa maso gabashin Afirka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI