Sojojin Sudan da mayakan RSF sun kashe fareren hula 176 cikin kwanaki biyu

Sojojin Sudan da mayakan RSF sun kashe fareren hula 176 cikin kwanaki biyu

Majiyoyin gwamnati da ƙungiyoyi dake sa’ido a rikcin Sudan ne suka bayyana wannan alƙaluman mutanen da hare-haren bangarorin biyu ya rutsa da su tsakanin ranakun Litinin zuwa Talata.

Harin RSF

A cewar gwamnan Khartoum Ahmed Othman Hamza, dakarun sa kai na RSF sun kashe akalla mutane 65 tare da raunata ɗaruruwa a Omdurman a ranar Talata.

Jami’in ya ce a wani harin mayakan a kan wata motar Bus ta safa-safa kadai ya kashe ɗaukacin fasinjoji da suke cike tare da gunduwa kunduwa da sassan jikin mutane 22.

Harin sojojin gwamnati

Harin na ranar Talata na zuwa ne, kwana guda bayan wani hari da jiragen yakin sojojin gwamnati suka kai kan wata kasuwa a garin Kabkabiya da ke arewacin Darfur, wanda ya kashe sama da mutane 100.

Cikin wata sanarwa da ƙungiyar lauyoyin gaggawa da ke fafutukar kare ƴancin bil’adama dake sa ido a rikicin Sudan, ta ce an kai harin ta sama ne a ranar da kasuwar mako-mako ta garin ke ciki, inda mazauna kauyukan da ke kusa da su suka taru domin yin siyayya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 100 tare da jikkata daruruwan da suka hada da mata da ƙananan yara..

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)