Adadin sojojin Majalisar Dinkin Duniya da aka kashe sakamakon harin ta'addanci a yankin Tumbuktu na Mali ya tashi zuwa 4.
Rundunar Sojin Ivory Coast ta sanar da cewa, karin sojanta 1 da ya jikkata sakamakon harin ya rasa ransa.
Sakamakon fashewar bam da aka dasa a hanyar Timbuktu-Duentza a lokacin da mitar sojojin MDD ta ke wucewa ne sojojin Ivory Coast 3 suka mutu nan take.