A farmakan da dakarun Masar suka kai a yankin Sina, sun samu nasarar kashe 'yan ta'adda 89.
Rubutacciyar sanarwar da Rundunar Sojin Masar ta fitar ta ce, ana ci gaba da kai farmakai a yankin Sina da ke arewa maso-gabashin kasar.
Sanarwar ta ce, a yayin kai farmakan an kashe 'yan ta'adda 89.
Haka zalika sanarwar ta bayyana an gano tare da rusa wasu hanyoyin karkashin kasa 13 da 'yan ta'addar suka yi amfani da su wajen kokarin shiga yankin Sina.
Sanarwar ta kuma ce, an kashe ko jiikkata sojojin Masar 8 a yayin kai farmakan.
A watan Fabrairun 2018 ne sojojin Masar suka fara kai farmakai ta sama, kasa da ruwa kan 'yan ta'adda a yankin Sina.