Sojojin Mali sun ce sun magance harin da aka kai Bamako

Sojojin Mali sun ce sun magance harin da aka kai Bamako

Rundunar sojin ƙasar tana gudanar da aikin tabbatar da tsaro bayan fafatawar da ta yi da ƴan bindigar da suka ƙaddamar da farmaki kan wata Cibiyar Ƴan sanda a Bamako.

A sanyin safiyar wannan Talatar ce, ƴan bindigar suka kai farmakin a kusa da filin jiragen sama kamar yadda wasu da suka shaida lamarin suka bayyana, inda suka tabbatar cewa, lallai sun ji ƙarar harbe-harbe da fashe-fashen bama-bamai.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya rawaito cewa, an kulle filin jiragen saman na wani  ɗan lokaci sakamakon fargabar abin da ka iya faruwa.

Tuni rundunar sojin ƙasar ta buƙaci mazauna yankin da su yi ƙaura na wucen-gadi kafin fitar da wata sabuwar sanarwa nan gaba.

Shugaban mulkin sojin Mali  Assimi Goita Shugaban mulkin sojin Mali Assimi Goita REUTERS - Mahamadou Hamidou Kazalika an tura wa ma'aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya da ke yankin da su takaita zairga-zirgarsu a halin yanzu.

Tun bayan juyin mulkin 2021, gwamnatin mulkin sojin Mali ke yaƙi da ƙungiyoyin ƴan ta'adda da suka haɗa da ƴan aware da mayaƙan jihadi masu alaka da al-Qaeda da ISIL.

A ƙarƙashin jagorancin shugaban mulkin sojin Mali, Kanar Assimi Goita, ƙasar ta yanke hulɗa da aminanta na ƙasashen Turai da kuma tsohuwar uwargijiyarta, Faransa, inda ta karkata hankalinta kan kulla alaƙa da Rasha da sojojin haya na Wagner domin samun agaji a fannin yaƙi da ƴan ta'adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)