A yayin da arangamar da aka fara a ranar 18 ga Disamba ke ci gaba a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sojojin kasar 117 sun gudu tare da neman mafaka a Kamaru.
Gwamnan yankin kudancin Kamaru Gregoire Mvongo ya shaida cewar, bayan an karbe makaman da ke hannun sojojin an kai su garin Garoua-Boulai tare da ajje su.
Bayan da kotun kolin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ta haramta takara ga tsohon Shugaban Kasar Francoi Bozize sakamakon samun sa da aikata laifukan yaki da majalisar Dinkin Duniya ta yi ne aka samu arangama tsakanin jami'an tsaron gwamnati da 'yan tawaye masu dauke da makamai.