Dakarun Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kusan kaso 80 din ta ke karkashin 'yan tawaye, sun sake kwato garin Cantonnier da ke iyaka da Kamaru, bayan kubutar da garuruwan Bouar, Boali, Bossembele da Yoleke daga hannun 'yan tawayen.
Labaran da jaridun kasar suka fitar sun ce, dakarun na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ke samun taimako daga sojojin Rasha da Ruwanda sun kwace iko da garin Contonnier.
A farmakan da dakarun Rasha suke bayar da taimako ta sama, sojojin gwamnati sun kwace garin da ke hannun 'yan tawaye masu kiran kansu da 'yan kishin kasa(CPC) ba tare da wata tangarda ba.
Kwanaki 2 da suka gabata sojojin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun kwace garin Bouar na kasuwanci wanda ya hada Banjui Babban Birnin Kasar da Kamaru wanda ke kan hanyar RN3.
A ranar 18 ga Disamban 2020 ne aka fara samun arangama tsakanin 'yan tawaye da sojojin gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya bayan da Kotun Koli ta haramtawa hambararren Shugaban Kasar Francois Bozize tsayawa takara saboda tuhumar sa da aikata laifukan yaki da kuma yadda Majalisar Dinkin Duniya ta saka masa takunkumai.