Rundunar Sojin Chadi ta sanar da kawo karshen yaki da 'yan tawaye 'yan a aware dake arewa maso-yammacin kasar.
Shugaban Rundunar Sojin Chadi Abakar Abdulkarim Daoud ya fitar da rubutacciyar sanarwar cewa, tun daga ranar 11 ga Afrilu suke gwagwarmaya da 'yan tawayen FACT a arewa maso-yammacin kasar, kuma yakin ya zo karshe bayan nasarar da sojoji suka yi.
Daoud ya kuma ce, jama'ar Chadi sun tarbi sojojin kasar a birnin Ndjamena cikin murna da farin ciki, kuma an kama 'yan tawaye 156 tare da kwace motocin yaki 17 da makamai da dama.
Daoud ya kara da cewa, an kama Mahdi Bashar wanda ya jagoranci hare-haren 'yan tawayen na FACT, kuma daga cikin 'yan tawayen akwai 'yan kasashen Libiya, Nijar da Sudan, wasunsu ma ba su fi shekaru 15 zuwa 16 ba.