Sojojin Burkina Faso sun ce sun dakile harin da aka kai a birnin Djibo

Sojojin Burkina Faso sun ce sun dakile harin da aka kai a birnin Djibo

Inda suka ce da sanyin safiyar Asabar, wasu mutane da dama dauke da makamai sun yi kokarin shiga cikin birnin kafin daga bisani aka fatattake su.

Wata majiyar tsaro ta ce an samu "kutsawar wasu masu ikrarin jihadi dakarun suka yi musu dirar mikiya kuma samu shawo kan lamarin bayan fatattakar su da akayi.

Wata kungiyar da ke da alaka da Al-Qaeda ce da aka fi sani JNIM mai ta da ƙayar baya a yankin, ta bayyana cewa da farko a ranar Alhamis ta karbe iko da wasu sansanonin soji da ke birnin Djibo.

Wannan dai ba shi ne karon farko da kungiyoyin da ke dauke da makamai suka kai wa Djibo hari ba, a cewar wadanda ke kewaye da birnin da wasu yankuna a lardin Soum da ke kan iyaka da kasar Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)