Sojojin Amurka sun kaiwa 'yan ta'addar Al-Shabab farmakai a Somaliya.
Kakakin Pentagon Cindi King ya shaida cewa, an kai farmakan ta sama kan 'yan ta'addar Al-Shabab a yankin Galkayo da ke da nisan kusan kilomita 700 daga Mogadishu Babban Birnin Somaliya.
Sanarwar ta ce, "Sakamakon yadda sojojin Somaliya da 'yan ta'addar Al-Shabab suke ci gaba da harar juna ba a iya gano asarar da aka yi ba, amma kuma ba a jikkata ko kashe farar hula ba a farmakan."
An bayyana an kai farmakin da hadin gwiwar Rundunar Sojin Somaliya da Rundunar Tsaron Amurka a Afirka (AFRICOM).