A kasar Mali da ke nahiyar Afirka, sojoji sun tsare manyan jami'ai da dama, ciki har da shugaban gwamnatin rikon kwarya, Bah Ndaw da Firaminista Moctar Ouane.
Labaran da kafafan yada labaran kasar suka rawaito na cewa, Ministan Tsaron kasar na cikin wadanda aka tsare kuma an kai su wani sansanin soja da ke Kati, wani yanki a wajen Bamako, babban birnin kasar.
A ranar 18 ga Yuni ne aka yi juyin mulki a Mali yayinda aka tsare shugaba Ibrahim Boubacar Keita kuma aka kafa sabuwar gwamnati.
A gefe guda kuma, Ofishin Jakadancin Turkiyya da ke Bamako ya gargadi Turkawan da ke zaune a Mali ta shafinsu na Twitter da cewa kada su fita kan tituna sai dai idan ya kama dole kuma su yi taka tsan-tsan.