Sojoji a Nijar sun dakatar da watsa shirye shiryen gidan talabjin na Canal3

Sojoji a Nijar sun dakatar da watsa shirye shiryen gidan talabjin na Canal3

Haka ma gwamnatin ta soke takarda aikin da aka  bawa baban Editan gidan jaridar Seini Amadou na tsawon watanni uku.

Ministan harakokin  sadarwa kasar Mohamed Raliou ya sanar da matakin ta cikin wani kuduri da ya rattabawa  hannu jiya alhamis ba tareda yin wani cikakken bayani ba.

Sai dai masu majiyoyi na kusa da gidajen radiyoyi a kasar ta Nijar na cewa, matakin baya rasa nasaba da wani rahoton da gidan talabijin din ya shirya wanda  ya karade shafukan sada zumunta inda aciki Editan Jaridar ya auna kuzarin ministocin gwamnatin rikon kwarya soji tareda rarrabawa kowanensu maki daidai da kwarewar shi  ta fuskar gudanar da aiki a gwamnati.

Tuni dai kungiyar masu kamfanonin sadarwa sukayi Allah wadai da matakin tareda yin kira ga minista da ya gaggauta sake duba matakin da ya dauka

A watan Disamba 2024 Jamhuriya Nijar ta dakatar da watsa shirye shiryen rediyo na BBC a tashoshin FM a fadin kasar na tsawon watanni uku.

Ko a farkon watan Augustan 2023, yan kwanaki bayan kwace mulkin da sojoji sukayi sun sakatar da watsa shirye shiryen rediyon RFI da talabijin na France 24 na Faransa bisa zargin nema tada zaune tsaye

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)