Sojin Sudan sun zargi mayakan RSF da amfani da kasar Chadi wajan kai musu hari

Sojin Sudan sun zargi mayakan RSF da amfani da kasar Chadi wajan kai musu hari

Ministan harkokin wajen Sudan ya faɗawa manema labarai a Port Sudan cewa, bincike ya tabbatar musu da waɗannnan jirage marasa matuƙa an ƙera su ne a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, kuma an harbo su daga Chadi da ke makwabtaka da iyakar Sudan.

Sudan dai na fama da rikice-rikice tun watan Afrilun 2023, tsakanin sojinta ƙarkashin shugaba Abdel Fattah al-Burhan da dakarun ƙungiyar agaji ta RSF.

A taron manema labarai da sojin suka gudanar jiya Litinin, sun nuna wasu hotunan jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami, wanda suka ce an harbo su daga filin jirgin sama da yankin iyaka a Chadi makon da ya gabata.

A shekarar 2023 da ta gabata, masanan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta samar domin tabbatar da haramcin harba makamai a Darfur, sun tabbatar da zarge-zargen da ake yi wa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na turawa dakarun RSF makamai ta Chadi.

Sai dai Haɗaɗɗiyar Daular Larabawar ta sha musanta taimakawa dakarun RSF a yaƙin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)