Aƙalla watanni 5 birnin ya yi ƙarƙashin ikon mayaƙan na RSF birnin da ke matsayin mahaɗa tsakanin yankin da yanzu haka ke hannun mayaƙan na RSF da kuma sauran sassan Sudan da ke ƙarƙashin ikon gwamnatin ƙasar.
Sanarwar da rundunar Sojin ta Sudan ta fitar a yau Asabar ta ce birnin Sinja hya kuɓuta daga hannun maƙiyan ƙasa RSF, sanarwar da ke zuwa dai dai lokacin da yaƙin na Sudan ke cika watanni 19 da farawa kuma ake ci gaba da tafka asarar ɗimbin rayuka.
Wani bidiyo da Sojin na Sudan suka wallafa a shafinsu ya nuna yadda dakarun ƙasar suka bazu a sassan birnin bayan karɓe iko da shi.
A gefe guda ministan yaɗa labaran ƙasar Khaled al-Aiser a wata sanarwa da ya fitar da kuma saƙon da ya wallafa a shafinsa ya bayyana cewa Sinja ya dawo ƙarƙashin ikon gwamnati.
Bayanai sun ce tuni shugaba Abdel Fattah ak-Burhan ya yi tattaki zuwa birnin na Sinja mai tazarar kilomita 60 daga arewaci don ganewa idonsa nasarar da dakarun ƙasar suka yi tare da gudanar da bikin murnar ƙwato birnin tare da su.
A watan Yunin da ya gabata ne RSF ta ƙwace iko da Sinja wanda ya tilastawa fararen hula aƙalla dubu 726 barin matsugunansu.
Yanzu haka dai RSF ke riƙe da ikon kusan dukkanin yankunan yammacin Darfur baya ga wani yanki na Kordafan da kuma wani kaso na birnin Khartoum sai kuma kudancin jihar Al-Jazira.
Tun bayan ɓarkewar yaƙin a watan Aprilun 2023 majalisar ɗinkin duniya ta ce dukkanin ɓangarorin biyu sun aikata laifuka da suka ƙunshi kisan mutanen da basu ji basu gani ba baya ga tilastawa wasu barin matsugunansu.
Alƙaluman Majalisar ɗinkin duniya sun ce dubban ɗaruruwan mutane ne suka rasa rayukansu a rikicin na Sudan yayinda fiye da mutum miliyan 11 suka bar matsugunansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI