Sojin Somalia da na Habasha sun kai wa juna farmaki a Jubaland

Sojin Somalia da na Habasha sun kai wa juna farmaki a Jubaland

Wata sanarwar ma’aikatar harkokin wajen Somalia tun a jiya Litinin ta ce Sojin Habasha sun farmaki dakarun nata da ke iyakarta ta Doolow a Jubaland da misalin ƙarfe 10 na safiyar jiya.

Duk da cewa Somalia ba ta bayyana alƙaluman mutanen da suka mutu a wannan hari ba amma ta ce hare-haren na Habasha sun shafi sansanoninta 3 da suka ƙunshi na Soji da na ƴan sanda da kuma sashen tsaron sirri waɗanda ke tare da sauran jami’an tsaro wanda ya haddasa asarar ɗimbin rayuka.

Dakarun na Habasha waɗanda ke da sansani jiragen yaƙi a zirin da ke gab da kan iyakar ƙarƙashin sansaninsu na yaƙi da ayyukan ta’addanci a yankin, bayanan da mahukuntan Jubaland mai ƙwarya-ƙwaryar ƴanci suka fitar sun ce suna kan hanyarsu ne ta bayar da kariya ga wata tawagar ƴan siyasar yankin lokacin da suka tashi a Shakwafta.

Ministan tsaro na Jubaland Yusuf Hussein ya ce tun farko Sojin na Somalia su ne suka nufaci harbo jirgin da ya tashi bisa umarnin gwamnatin Mogadishu lamarin da ya kai ga musayar wuta tsakaninsu da dakarun Addis Ababa.

Tun gabanin wannan faɗa, tsawon makwanni aka shafe ana kai ruwa rana tsakanin Sojin Somalia da dakarun jihar ta Jubaland mai ƙwarya-ƙwaryar ƴanci dangane da haƙƙin mallakar wasu yankuna masu muhimmanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)