
Rahotanni sun ce aƙalla mutane 9 daga cikin magoya bayan Imam Dicko ne aka kame tare da jefasu a gidan yarin birnin Bamako jiya Laraba, bayan da aka tuhumesu da taruwa ba bisa ƙa’ida ba.
A cewar bayanai tun a ranar 14 ga watan da muke ciki ne, magoya bayan na Imam Dicko suka yi dafifi da nufin tarbarshi, amma kuma ya fasa zuwa ƙasar saboda wasu dalilai, sai dai tun daga wancan lokaci ne sojojin da ke mulkin ƙasar ta yammacin Afrika ke ci gaba da kamewa tare da tsare ɗimbin magoya bayan nasa.
Bayanan sun ce galibin waɗanda suka yi dafifi zuwa filin jirgin saman na Bamako a lokacin tarbar malamin, masu adawa ne da jagorancin da Sojoji ke yi a ƙasar.
Kafin yanzu akwai alaƙa mai kyawu tsakanin Imam Mahmoud Dicko da gwamnatin Sojin ta Mali, sai dai baya-bayan nan sun samu farraƙa ta yadda ya komawa ɗan adawa mafi girma ga tafiyar Sojojin.
Dicko na cikin waɗanda ke tsananta kiranye-kiranye ganin an rushe gwamnatin Sojin don gudanar da zaɓe, lamarin da bai yiwa Sojojin daɗi ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI