Ƴan tawayen M23 sun kama birnin Goma mafi girma a yankin gabashin kasar ne a wannan mako, bayan yiwa sojojin gwamnati da kuma sojojin hayar kofar rago a Tafkin Kivu dake kusa da iyakar Rwanda.
Rahotanni sun ce sojojin hayar ganin an musu kawanya sun aje makamansu ba tare da fafata yaki ba, inda suka mika kan su ga dakarun majalisar dinkin duniya wadanda suka shirya musu hanyar kwashe su zuwa kasar su ta cikin Rwanda.
Sojojin hayar Romania da Congo ta ɗauko © ReutersKamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito daya daga cikin sojojin hayar da ya tabbatar da cewar shi 'dan kasar Romania na bayyana farin cikin sa na komawa gida.
Rwanda ta sake watsi da zargin da ake mata na goyawa 'yan tawayen M23 baya, inda tace tana daukar matakan kare kan ta ne, yayin da ta zargi Congo da hada kai da wadanda suka aikata kisan kare dangi a shekarar 1994.
Bayanai sun ce Congo ta dauko sojojin hayar Romania ne domin taimakawa dakarun ta wajen sarrafa jirage marasa matuka wadanda sojojin Rwanda ke kakkabowa.
Sojojin hayar Romania da Congo ta ɗauko © ReutersRahotanni sun ce Congo ta dauki hayar kamfanin Agemira RDC, wanda wani reshe ne na kamfanin kasar Bulgaria domin tabbatar da tsaro a cikin kasar ta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI