Shugabannin wucin gadi na Mali sun yi murabus

Shugabannin wucin gadi na Mali sun yi murabus

Shugaban Gwanatin Wucin Gadi ta Mali Bah N'Daw da Firaministan Kasar Moctar Ouane sun yi murabus.

Sakataren Musamman na Mataimakin Shugaban Gwamnatin Wucin Gadi ta ta Mali Assimi Goita, baba Cisse ya shaidawa 'yan jaridu cewa, N'Daw da Ouane sun yi murabus tare da barin aiyukansu.

Cisse ya kara da cewa, ana ci gaba da tattaunawar kasa da kasa don ganin san saki N'Daw da Ouane da kuma kafa sabuwar gwamnati.

A ranar Litinin din nan ne Goita ya sanar da cire Shugaban Gwamnatin Wucin Gadi da Firaministan Mali sakamakon karya ka'idojin tafiyar da gwamnati inda ska kafa sabuwar majalisar zartarwa. Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta tura wakili Mali don shiga tsakani.

Bayan sanarwar yin sauye-sauye a majaliisar zartarwa ta Mali a ranar 24 ga Mayu ne sojojin kasar suka kama manyan Shugabannin gwamnati da suka hada da Shugaban Wucin Gadi N'daw da Firaminista Ouane.

Ba a nada tsohon Ministan Shari'a Kanal Sadio Camara da tsohon Ministan Tsaro Kanal Modibo Kone a sabuwar majalisar Ministocin da aka kafa ba. Ana ikirarin cewa, Camara da Kone ne suka yi juyin mulkin ranar 18 ga Agustan 2020.

A ranar 18 ga Agustan 2020 ne aka kifar da gwamnatin Mali karkashin Ibrahim Boubacar Keita inda sojoji suka kafa Gwamnatin Wucin Gadi.


News Source:   ()