Tun bayan bullar ta a shekarar 2021 mayakan M23 da ke samun goyon bayan Kigali, wadanda ke ikirarin kare kabilar Tutsi, sun kwace iko da yankuna na DRCongo, tare da raba dubbai da gidajen su da kuma haddasa rikicin tsakanin kabilun yankin.
A farkon watan Agusta, Angola ta shiga tsakani a wannan rikici da zimar samar da mafita tsakanin kasashen biyu.
Angola na fatan cimma daidaita al'amura a fagen daga, amma bangarorin biyu sun ci gaba da musayar wuta, kuma fadan ya kara tsananta tun karshen watan Oktoba. Shugaban Angola Joao Lourenco, wanda kungiyar Tarayyar Afirka ta nada a matsayin mai shiga tsakani, ya bayyana fatansa jiya Alhamis cewa taron da za a yi a Luanda zai kai ga cimma yarjejeniyar zaman lafiya. Lourenco ya ce, "Muna da kwarin gwiwar cewa, a karshe wannan taron zai kai kasashen biyu ga rattaba hannu ko yanke shawarar kulla yarjejeniyar zaman lafiya mai dorewa.
Shugaban na Angola ya bayyana cewa shugaban kasar Rwanda Paul Kagame zai halarci taron na ranar Lahadi. Fadar shugaban DRCongo ta kuma tabbatar da cewa Felix Tshisekedi zai kasance a wannan taro, duk da kin amincewa da DRCongo a baya na yin shawarwari da Rwanda da kuma kiran da ta yi na a kakaba mata takunkumin kasa da kasa kan makwabciyarta.
Tshisekedi ya fada a majalisar dokokin kasar jiya Laraba cewa, "Kasarmu na ci gaba da fuskantar 'yan tawaye masu ci gaba, ciki har da hare-haren wuce gona da iri na sojojin kasar Rwanda da 'yan ta'addar M23." Babban birnin lardin Kivu ta Arewa na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Goma, mai mutane kusan miliyan daya da kuma wasu miliyan guda da yaki ya raba da muhallansu, yanzu haka yana kusa da 'yan tawayen M23 da sojojin Rwanda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI