Shugabannin Afrika za su gudanar da taro don cimma matsaya kan bautar da al'ummarsu

Shugabannin Afrika za su gudanar da taro don cimma matsaya kan bautar da al'ummarsu

Babbar dalilin bijiro da wannan batu shi ne, neman ƙasashen da suka yi wa Afirka mulkin mallaka su gyara kura-kuran da suka yi a tarihi, lura da irin mummunan tasirin da bautar da ɗan Adam ya yi ga rayuwa da kuma tauye ci gaba musamman nahiyar ta Afirka.

A daidai lokacin da wannan batu na biyan diyya ke ci gaba da samun karbuwa a duniya, sai haka kwatsam shugaban Amurka Donald Trump ya fito yana cewa ‘’Ba na zaton cewa batun biyan diyyar wani abu ne mai yiyuwa”. Hakazalika wasu daga cikin shugabannin Turai na nuna adawarsu da wannan batu.

To sai dai duk da wannan ƙalubale, shugabannin na Afirka za su tattauna tare da cimma matsaya da kuma gabatar da buƙatar ganin waɗanda suka bautar da jama’asu sun amince da laifukansu na baya, daga nan kuma sai irin diyyar da ya kamata a biya.

Alƙalumma sun tabbatar da cewa daga ƙarni na 15 zuwa na 19, aƙalla mutane majiya ƙarfi milyan 12 da dubu 500 dukanninsu ƴan Afirka ne aka kwashe zuwa Turai da Amurka domin bautar da su, lamarin da ake ganin shi ne ya ƙara jefa Afirka a cikin halin ƙunci saboda yadda aka raba nahiyar da majiya ƙarfi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)