Shugabannin Afirka sun sha alwashin kare al'adu da kayan tarihin nahiyar

Shugabannin Afirka sun sha alwashin kare al'adu da kayan tarihin nahiyar

Shugabannin Afirka sun kammala taron da suka gudanar karo na 34 da nufin tattauna aiyukan yaki da annobar Corona da kuma kare al'adu da kayan tarihi na nahiyar.

Shugaban Tarayyar Afirka kuma Shugaban Kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo Felix Tshisekedi ne ya yi jawabin rufe taron.

A jawabin nasa ya bayyana cewa, duk al'umar da ba ta da al'adu, to ba ta da rai, kuma ya yi alkawarin zai bayar da goyon baya wajen sake gina Tsibirin Gora na Sanagal, Babban Gidan Adana Kayan tarihi na Afirka da ke Aljeriya, Babban Gidan Adana Kayan Tarihi na Masar da sauran wuraren da ke dauke da al'adun nahiyar.

Tshisekedi ya kuma bayyana cewar, za su bukaci a dawowa da Afirka dukkan kayayyakinta na tarihi da suke ajje a kasashen Turai.

Shugaban na Tarayyar Afirka ya kuma ci gaba da cewa, za su aiwatar da sabbin aiyuka da za su gaggauta fara aiki da yarjejeniyar kasuwanci ta Afirka, kuma zai gudanar da aiyukan ganin kasashen Masar, Itopiya da Sudan sun kawo karshen sabanin da suke yi kan Madatsar Ruwa ta Hedasi.


News Source:   ()