A shari'ar farko da kotun ta ICC ta yi na duba irin ta'asar da ake zarginsa da aikatawa a Darfur, masu gabatar da kara a farkon makon nan sun ce Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman shi ne shugaban kungiyar Janjaweed da aka fi sani da nom de guerre Ali Kushayb wanda ya jagoranci mayakan da ke goyon bayan gwamnati wajen fada a tsakanin shekara ta 2003-2004.
Ya kuma ce shi ba shine ba Ali Kushayb da ake nema ba ne, kuma bai san wannan mutumin ba, abin da Abd-Al-Rahman ya shaida wa alkalai kenan a karshen shari'ar ta sa.
Wanda ake tuhumar ya ce a shekarar 2020 ne da kan sa ya mika kansa ga kotu domin ya wanke sunansa, inda ya ce ba shi da alaka da tuhumar da ake masa.
Sannan Lauyoyin Abd-Al-Rahman suka yi kira da a wanke shi daga zargin da ake masa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI