Rahotanni daga kasar na nuni cewa Madouri sabon Firaministan kasar ta Tunisia ya dauki nauyin harkokin zamantakewa ne kawai a watan Mayu na wannan shekara. A wani sako da aka wallafa a shafin sada zumunta na yanar gizo daga ofishin Shugaban kasar ta Tunisia, an nuna Saied yana jijinawa Madouri tare da takaitaccen bayani.
Shugaban kasar ta Tunisia Saied, mai shekaru 66, wanda aka zaba a shekarar 2019 amma ya kitsa yunkurin kwace madafun iko a shekarar 2021, kuma a yanzu yana neman wani wa'adin mulki a zabe ranar 6 ga Oktoba.
Shugaban Tunisia Kais Saied © Fethi Belaid / AFPA farkon makon nan ne ya shigar da bukatarsa na tsayawa takara a hukumance, yayin da kungiyoyi da yan adawa ke kokawa ganin ta yada aka hana wasu yan siyasa damar shigar da bukatar tsayawa takara.
Shugaban kasar ta Tunisia ya shaida wa manema labarai cewa takararsa wani bangare ne na tabbatar da kuma kwato ‘yancin gashin kai" da nufin "kafa sabuwar jamhuriya".
Magoya bayan Shugaban Tunisia © FETHI BELAID / AFPDaga cikin masu adawa da Shugaban kasar ta Tunisia, Abir Moussi, babbar ‘yar adawa kuma tsohuwar ‘yar majalisar dokokin kasar da ke gidan yari tun a watan Oktoba,wacce aka yankewa hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari bisa tuhumar ta da laifin sabawa dokokin kasar ta mika takarar ta ta hannun lauyoyinta.
An kuma yankewa wani dan jarida Nizar Chaari hukuncin watanni takwas a daren litinin, kwanaki bayan da aka kama wasu ma’aikatan yakin neman zabensa guda uku bisa zarginsu da keta dokoki da suka jibanci bangaren saka hannu aa takardun neman takara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI