Shugaban sojojin Uganda ya yi barazanar fille kan jagoran adawar ƙasar

Shugaban sojojin Uganda ya yi barazanar fille kan jagoran adawar ƙasar

Muhoozi Kainerugaba da ake kyautata zaton shi zai gaji mahaifinsa, da ke mulkin ƙasar Uganda tun daga shekarar 1986 ya saba yin rubuce-rubuce masu tayar da hankali a shafukan sada zumunta, ciki har da barazanar mamayar makwabciyar Kenya a shekarar 2022.

Ko da yake daga baya Kainerugaba ya nemi afuwa kan wannan barazana da ya wallafa, yana mai cewa wani lokaci ana tauna tsakuwa ce.

A wani sakon da ya wallafa a ranar Lahadi da yamma, Kainerugaba ya ce in ba don mahaifinsa na kare jagoran ƴan adawa Bobi Wine ba da tuni ya hallaka shi.

Bobi Wine, wanda sunansa na ainihi Robert Kyagulanyi wanda ya zo na biyu a kan Museveni a zaɓen shugaban kasa na shekarar 2021, ya mayar da martani a shafin X cewa bai ɗauki barazanar da wasa ba, yana mai cewa an yi yunkurin kashe shi a baya.

A martaninsa ga Wine Kainerugaba ya bayyana cewa:

ka biya ƙudin da muka ranta maka kafin ga cika baki 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)