Shugaban sojin Sudan ya fasa shiga tattaunawar sulhu da 'yan tawayen RSF

Shugaban sojin Sudan ya fasa shiga tattaunawar sulhu da 'yan tawayen RSF

Janar Abdul Fatah Albrhan ya sanar da janyewa da daga shiga tattaunawar ce kwanda guda bayan da ya tabbatar da aniyarsa ta halartan zaman sulhun da Amurka da shirya a Geneva na ƙasar Swizland, sakamakon harin na maraicen Laraba.

Rundunar sojin Sudan ta ce mutane 5 ne suka mutu a harin da jirgin yaki mara matuki ya kai sansanin soji dake Gibet, inda Janar Burhan ya halarta domin bukin yaye dalibai, a garin nisan kilomita 100 daga birnin Port Sudan mai tashar jiragen ruwa.

An ga shugaba Burhan cikin kwoshin lafiya jim ƙadan bayan harin, yana cewa irin wannan hari na kurman jirgi bazai razana shi ko ya sa ya bada kai ba.

Wannan harin na zuwa ne, bayan da bangarorin  biyu da basa ga maciji da juna wato na sojojin gwamnati da Janar Alburhan ke jagoranta da tsohon mataimakinsa Janar Hamdan Daglo dake jagorantar dakarun sakai na RSF suka amince da gayyarata Amurka domin zaman tattaunawar zaman lafiya a Geneva a cikin watan Agustan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)