Rahotanni sun ce mafi yawan alƙalan da suka bada gudunmowa a sharia’ar zargin yiwa mata fyaɗe da aka yiwa Prime ministan ƙasar Ousmane Sonko an sauya musu guraren aiki zuwa wajen birnin Dakar.
An mayar da babban alƙali da ke sanya idanu kan ayyukan alƙalan babbar kotun birnin Dakar Oumar Maham Diallo zuwa yankin Tambacounda matsayin jagoran alƙalan yankin.
Shi kuwa Abdou Karim Diop babban mai gabatar da ƙara da ya gurfanar da Sonko a gaban shari’a kan laifuka da dama ciki har da sata ya gamu da sauyin aiki zuwa babban antoni janar na kotun ɗaukaka ƙara a yankin Tambacounda, kuma an tura su chan ne tare da Mai shari’a Mamadou Seck tsohon alƙalin babbar kotun birnin Dakar.
Ana dai ganin wannan wani salo ne na hukunta alƙalan kan hukuncin da suka yankewa ubangidan sa, sai dai kuma yayin sanar da sauyin gurin aikin Faye yayi kalamai da ke nuna cewa sauyin bashi da wata alaƙa da siyasa ko kuma biyan bukatar wani mutum.
Garin Tambacounda, yayi ƙaurin suna tsakanin ma’aikatan ƙasar ta yadda basa son a turasu chan sakamakon rashin kayayyakin more rayuwa, nisa da babban birni da kuma tsananin zafi da ake fama da shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI