Bayan ziyartar Faransa, Shugaban Majalisar Gudanarwa ta Libiya Muhammad Al-Manfi na ziyara a Alkahira Babban Birnin Masar.
Masar ce kasar waje ta biyu da Al-Manfi ya ziyarta.
Sanarwar da aka fitar daga Sashen Sadarwa na Majalisar ta ce, Manfi, mataimakinsa Abdullah Al-Lafi da 'yan tawagarsu sun ziyarci Alkahira.
Sanarwar ta ce, an kai ziyarar a karkashin alaka mai tarihi da ta hada kasashen 2, kuma ana da manufar kara karfafa dangantakar kamar yadda jama'ar Libiya da Masar ke bukata.
A gefe guda, wani jami'in ofishin da ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa, za a yi ganawa ta musamman a yayin ziyarar.
Jami'in ya ce, bayan ziyartar Masar, Manfi da 'yan tawagarsa za su wuce zuwa Turkiyya.
A Taron Neman Mafitar Siyasa a Libiya da Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranta a ranar 5 ga Fabrairu, an zabi Manfi a matsayin Shugaba da Al-Dibaybi a matsayin Firaministan Libiya.
Bayan rantsar da Manfi, ya ziyarci kasar waje ta farko inda a ranar 23 ga Maris ya je Faransa.