
Kungiyar ta AU na da yakinin cewa, ba za a yi zabe ba, ba tare da an yi sulhu tsakanin bangarori dake dauke da makamai.
A ranar farko ta wannan ziyara, jami'an kungiyar AU sun gana da firaministan Tripoli Abdelhamid Dbeibah. A cewar dandali na gwamnati, shugaban kasar Mauritaniya Mohamed Ould Cheikh El Ghazouani ya tabbatar da cewa, babban kwamitin zai ci gaba da gudanar da ayyukansa na cimma daidaiton kasa.
A watan da ya gabata ne,bangarorin biyu suka sanar da sanya hannu, karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya, kan yarjejeniyar nadin sabon gwamnan babban bankin kasar, a tsakiyar rikicin mulki na sama da wata guda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI