Shugaban Kasar Uganda Yoweri Museveni da ya sake lashe zabe ya nada Ministoci 82.
An bayyana cewa, a sabuwar gwamnatin da aka kafa a Uganda akwai kananan Ministoci 50 da manya 32.
Museveni ya nada tsohuwar Ministar Lafiya Robinah Nabbanja a matsayin Firaminista, ya kuma nada matarsa Janet Museveni a matsayin Ministar Ilimi.
A ranar 14 ga watan Janairun 2021 ne Museveni ya sake lashe zaben Shugaban Kasar Uganda a karo na 6.
Museveni ya lashe zabuka a shekarun 1996, 2001, 2006, 2011, 2016 da 2021.