Shugaban Kasar Tanzania Magafuli ya rasu

Shugaban Kasar Tanzania Magafuli ya rasu

An bayyana rasuwar Shugaban Kasar Tanzaniya John Magafuli.

Mataimakiyar Shugaban Kasar Tanzaniya Samia Saluhu Hassan ta yi jawabi a tashar talabijin ta kasar cewa, "Mun rasa jajirtaccen Shugabanmu".

Hassan ta ce, tun ranar 6 ga Maris Magafuli ya kwanta a wani asibiti da ke Darussalam bayan samun matsala a zuciyarsa.

An sanar da zaman makoki na kwanaki 14 a Tanzaniya sakamakon mutuwar Shugaban Kasar.

Magafuli mai shekaru 61 ya lashe zaben Shugaban Kasar a karo na 2a watan Oktoban 2020.

Kwanaki 2 da suka gabata 'yan adawa a Tanzaniya sun bukaci da a fitar da sanarwa nan da nan game da Shugaban Kasar da aka dauki tsawon makonni 2 ba a ganin sa inda suke cewa ya kamu da cutar Corona.

Shugaban na Tanzaniya bai dauki cutar Corona da muhimmanci ba a saboda haka ba ya daukar matakan kariya, kuma a ranar 10 ga Maris ya je Kenya don yin maganin cutar.

Magafuli ya dinga baiwa jama'arsa shawaharar su dinga yi sirace, suna shan kayan marmari kuma ba ya saka takunkumi a wajen taruka.

A watan Fabrairu Sakataren Fadar SHugaban Kasar John Kijazi ya rasa ransa amma ba a fadi cutar da ta yi ajalin sa ba, haka kuma Mataimakin Shugaban Zanzibar Saif Sharif ma ya rasu bayan kamuwa da cutar Corona.

 


News Source:   ()