Shugaban Kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya mutu sakamakon bugun zuciya.
Sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar ta ce bayan da Nkurunziza ya buga wasan bolleyball a ranar Asabar ne ya fara rashin lafiyar da ta sanya aka kai shi asibiti.
An bayyana cewar a ranar Lahadi ya dan samu sauki, amma a ranar Talata sai lamarin nasa ya sake munana kuma duk kokarin likitoci na ceton ransa ya ci tura.
Sanarwar ta mika sakon ta'aziyya ga iyalan Nkurunziza da dukkan jama'ar kasar, za a sauke tutoci inda aka kuma aiyana zaman makoki na kwanaki 7 a kasar da ke gabashin Afirka.
Tun shekarar 2005 Nkurunziza ya hau karagar mulkin Butundi, kuma ya shirya don mika mulki a ranar 20 ga watan Agusta ga dan takarar jam'iyyarsa kuma amininsa Janaral Evarise Ndayishimiye wanda ya lashe zaben da aka gudanar a watan Mayis.