Shugaban Kasar Angola Joao Manuel Gonchalves Lourencho na ziyara a Ankara Babban Birnin Turkiyya sakamakon goron gayyatar da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya mika masa.
Shugaba Erdogan ya tarbi Laurencho a Fadar Gwamnati da ke Ankara.
Bayan shugabannin 2 sun gana da juna, an sanya hannu kan wasu yarjeniyoyi a tsakaninsu.
Bayan taron manema labarai, Erdogan ya shirya liyafar cin abincin dare tare da Lourencho.